(ABNA24.com) A karon farko cikin shekaru 23, Amurka za ta nada jakada a kasar Sudan, kamar yadda sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya sanar.
Sanarwar ta ce kasashen biyu sun sau matakin musayar jakadu bayan shafe tsawan shekaru 23, wanda ake kallo a matsayin wani babban ci gaba a gwamatin wucin gadin kasar ta Sudan.
A ranar Laraba data gabata ne firaministan kasar ta Sudan Abdallah Hamdok, ya gana da mukadashin sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka a birnin Washington, wacce kuma ita ce ziyara irinta ta farko ta wani babban jami’in Sudan tun bayan shekara 1985.
Alaka tsakanin Amurka da Sudan ta dai yi tsani a tsawan sheakru 30 na mulkin hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al-bashir, wanda sojoji suka kifar sakamakon boren jama’ar kasar na kin jinin gwamnatinsa..
A cikin shekara 1990 ne Amurka ta sanya Sudan a cikin jerin kasashen dake goyan bayan ayukan ta’addanci bayan data karbi shugaban kungiyar Al-Qaida Usama Ben Laden.
Gwamnatin Khartoum dai ta bukaci Amurka data cire ta daga cikin jerin kasashen data ayyana masu goyan bayan ta’addanci, lamarin day a durkusar da tattalin arzikinta.
Amurkart dai ta ce a shirye ta aiwatar da hakan idan an samu ci gaba, amma dai matakin zai dauki dan lokaci.
/129